16 Oktoba 2021 - 17:27
Iran Ta Karyata Kalaman Shugaban Azerbaijan Dangane Da Safarar Miyagun Kwayoyi

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sa’id KhadibZadeh ya karyawa maganganun shugaban kasar Azerbaijan, Ilham Aliyuf na baya-bayan nan, inda yake cewa Iran tana hada kai da kasar Armeniya wajen safarar miyagun kwayoyi zuwa kasashen turai.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shafin yanar gizo na ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya nakalto KhadibZadeh ya na cewa dubban shahidan da kasar Iran ta bayar don yaki da miyagun kwayoyi da kuma dubban jami’an tsaron kasar da suka ji rauni saboda hakan duk sun wadatar don karyata zancen shugaban.

Khadib Zadeh ya kara da cewa irin wadannan maganganun da Aliyuf ya yi, ba wanda zai amfana da su sai haramtacciyar kasar Isara’ila. Daga karshe kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya ce danganataka tsakanin gwamnatin Iran da ta Arzerbajan ta na da kyau.

342/